Kotu Ta bada umurnin a Saki Mubarak Bala a kuma biyashi kudi N250,000
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta ba da umarnin sakin Mubarak Bala, wani ma’abocin amfani da shafin Facebook da yake amfani da asusunsa wajen wallafa sakon da yake yi batanci ga addinin Islama da Annabi Mohammed (S.A.W).
Mubarak Bala, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar ‘rajin Yan Adam na Najeriya, an kame shi ne a cikin watan Fabrairu a gidansa dake Kaduna’ biyo bayan korafin da wasu lauyoyi suka gabatarwa hukumar 'yan sandan ta Jihar Kaduna.
An Zarge shi (ya tabbata) da yin batanci ga Annabi Muhammad a fili a shafinsa na Facebook.
'Yan sandan sun kuma dauke shi zuwa jihar Kano a ranar 2 ga Mayu ta 2020.
Yayin yanke hukunci a kan karar da Bala ya shigar na ikirarin hakkinshi ta hannun lauyan sa, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yanke hukuncin cewa kama Bala da tsare shi da ‘yan sanda suka yi kamar tauye masa‘ yanci ne na kansa, na ‘yancin tunani, ra’ayi, da sauransu.
"Hana shi damar ganawa da lauyoyinsa, ya zama babban take hakkine kakarshin sashi na 34 da 35 (2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999."
Alkalin ya kuma umarci ‘yan sanda da su biya shi jumular kudi N250,000 a matsayin diyya.
Mubarak Bala ya kasance mai sukar addini sosai bayan da aka ce ya bar addinin Islama a 2014.
Inda a baya cewa akayi danginsa sun yi tunanin ko ya haukacene suka garzaya dashi zuwa asibitin mahaukata dake a Kano amma daga bisani an sallame shi ya kuma ci gaba da sukar Addini har ya kaiga a ka mashi.
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Kotu Ta bada umurnin a Saki Mubarak Bala a kuma biyashi kudi N250,000"
Post a Comment