Maryam Booth ta lashe kyautar mataimakiyar Jaruma na AMAA Award 20


Maryam Booth ta lashe kyautar mataimakiyar Jaruma na AMAA Award 2020

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Maryam Booth ta tayi nasarar lashe kyautar mataimakiyar jaruma (supporting actor)  a bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy. 


Maryam Booth ta lashe kyautar ne dalilin rawar da ta taka a fim din: The Milkmaid, inda ta doke Chairmaine Mujeri (Mirage), Linda Ejiofor (Jamhuriya ta 4), da wasu mutane hudu. 

Don murnar samun kyautar, jarumar ta rubuta a shafinta na Instagram in da tace “Ina taya kaina murna tare da iyalina na fim din The Milkmaid. Fatan wasu nasarori. Zamu hadu nan ba da jimawa ba a Oscar. 

" Shima da yake taya ta murnar samun kyautar, jarumin da ya lashe lambar yabo, Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “Ina taya ku murnar samun lambar yabo ta Kwalejin Fim ta Afirka da ta fi dacewa da 'yar wasa mai goyan baya a Milk Maid. Wannan mafari ne, 'yata Maryam Booth. ” 

Taron, wanda aka gudanar kuma ranar Lahadi 20, Disamba 2020. Dan wasan kwaikwayo Lorenzo Menakaya ne ya shirya.

Film din 'The Milkmaid', Wanda ya rubuta kuma ya bada umarni shine Desmond Ovbiagele, shine  Najeriya ta gabatar a 2021 a Oscar.



Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "Maryam Booth ta lashe kyautar mataimakiyar Jaruma na AMAA Award 20"

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies