Hukumar NDLEA Ta Kama wata mata Da Hodar Iblis Ta N30bn
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Najeriya NDLEA, tayi nasarar kama wata mace da hodar iblis da ta kai darajar naira biliyan 30 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da keva Jihar Legas.
Mista Jonah Achema wanda shine Kakakin Hukumar, ya bayyana hakan ranar Asabar a birnin Abuja.
Cikin sanarwan Mista Jonah Achema ya ce anyi nasar cafke wannan hodan wacce nauyinta ya kai kilo 26.840 a hannun wata mata, mai suna Onyejegbu Ifesinachi Jennifer mai shekaru 33 da ta shigo Najeriya ranar Laraba daga birnin Sao Paolo na kasar Brazil.
A cewarsa, cikin shekaru 15 da suka wuce wannan ita ce hodar ibilis mafi nauyi da aka taba kamawa a kasar.
Acewarsa, “Matar da ake zargi mace mai gyaran gashi a Brazil kuma ta amsa cewa kwangila a ka bata na ta shigo da hodar kan cewa za a biya ladan naira miliyan biyu,” inji shi.
Haka zalika, ya ce matar bata ambaci sunayen wadanda suke aiki tare ba ko wadanda suka bata kwangilar, sai dai ta ce ita umarni aka bata kan ta mika hodar ga wani.
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Hukumar NDLEA Ta Kama wata mata Da Hodar Iblis Ta N30bn"
Post a Comment