Ciwo yafi saurin warkewa a duniyar sama fiye da duniyar kasa.
Wani Dan sama jannati dan asalin kasar Rasha mai suna Sergey Kud-Sverchkov ya shaida cewa, lalle ciwo ya fi warkewa da wuri a duniyar sama.
Kamfanin dillancin labarai na Sputnik ne ya bayyana sanarwar da dan kasar ta Rasha Sergey Kud-Sverchkov da ke aiki a tashar 'yan sama jannati ta kasa da kasa ya fitar ta shafinsa na Twitter.
A sanarwar dan sama jannatin ya ce "A wajena, ciwo ya fi warkewa a duniyar sama. Watakila dalilin hakan shi ne sabo da yadda babu kwayoyin cuta da yawa a sama, kuma sama da akwai iska busasshiya."
A tashar ta 'yan sama jannati ta kasa da kasa da akwai 'yan kasar Rasha biyu Sergey Kud-Sverchkov da Sergey Rikikov da kuma wasu Amurkawa hudu Kate Rubins, Michael Hopkins, Victor Glover da Shannon Walke sai kuma dan kasar Japan daya Soichi Noguchi da ke gudanar da aiyukan bincike.
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Ciwo yafi saurin warkewa a duniyar sama fiye da duniyar kasa."
Post a Comment