kotu ta hana Andrew yakubu miliyoyin daloli.

Wata babbar kotu a Kano ta
ki amincewa da bukatar da
ya tsohon manajan kamfanin
mai na Najeriya NNPC,
Andrew Yakubu ya shigar,
inda ya nemi da a watsar da umarnin da kotun ta bai wa
hukumar da ke yaki da masu
yi wa tattalin arzikin kasa
ta'annati cewa ta damkawa
gwamnatin tarayya kudin. A watan Fabrairu ne kotu ta
bai wa hukumar EFCC damar mallakawa gwamnati sama da dala miliyan 9.8 da aka samu daga gidan Mista Yakubu a Kaduna. Kun san abin da dalolin Andrew yakubu za su iya yi a Nigeria? EFCC ta kwato miliyoyin daloli a gidan tsohon shugaban NNPC Mai shari'a Zainab Abubakar ce
ta yanke hukunci kan bukatar
wadda lauyan Mista Yakubu ya
shigar, inda ta ce kotu tana da
hurumin sauraron karar ba
kamar yadda lauyan ya nuna cewa hakan ba daidai ba ne. Wakilin BBC a Kano ya ce mai
shari'ar ta kuma ce bukatar
Mista Yakubu da ke neman a yi
watsi da shari'ar ba ta da wata
madogara a shari'ance, kuma
dokar kasa ta bai wa EFCC damar neman umarnin a mika
kudin ga gwamnati. Tuni EFCC ta fara tuhumar
tsohon shugaban NNPC din a
kan kudaden da aka samu a
gidan nasa.

Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "kotu ta hana Andrew yakubu miliyoyin daloli."

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies