An tsawaita wa'adin hada nambar NIN da layukan wayan salalu

 
Gwamnatin Nigeria ta sake tsawaita wa’adin da ta diba  wa yan kasar domin hada lambar katin  su ta  dan kasa (NIN) da layukan waya har  na tsawon karin makonni takwas.
Gwamnatin Nigeria ta sake tsawaita wa’adin da ta diba  wa yan kasar domin hada lambar katin  su ta  dan kasa (NIN) da layukan waya har  na tsawon karin makonni takwas.

Dagewar  da akayi  na nufin za a ci gaba da yin rijistar ne har nan da ranar shida ga watan Afrilun 2021.

Da kansa ministan Sadarwa, ta Nigeria Dr Isa Ali Pantami shi ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da yayi yayin da yake tattaunawa da wani Kwamitinsa na Kar-ta-kwana kan tabbatar da hada layukan da ya gudana a Abuja ranar Litinin.

Dr Pantami ya ce an yanke shawarar yin ha kan ne saboda a ba wasu dimbin ‘yan kasar da ma baki dake zaune cikin Nigeria a kan ka’ida damar samun yin hakan.

Akwai sama da mutane miliyan 56 Ya zuwa yanzu da kamfanonin layukan waya suka sami nasarar hada lambobin NIN dinsu da layukan wayoyin nasu.

Mininistan na sadarwa Dr Pantami cikin sanarwar yace “ za a iya hada Kowacce lambar NIN da akalla layuka uku zuwa hudu.

Ya kuma ce “Lalle an sami karuwa matuka a alkaluman da muka Sami nasaran tattarawa, mun sami karin adadin mutane miliyan 47 ya zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2021,”.

Haryanzu cikin sanarwar ta yace da akwai akalla cibiyoyin yin rijistar katin dan kasa guda 1,060 a fadin kasar gaba ki daya mallakan gwamnati, sannan su kuma kamfanonin wayar sun bude daruruwan cibiyoyin yin hakan a fadin kasa.

Ministan ya ce  shirin rijistar shirine  daga cikin shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarinsa na  inganta tsaron kasar da kuma saukakawa mutane domin su sami hada lambobin cikin sauki.

A watannin baya ne dai Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa (NCC) ta fitar da sanarwan barazanar rufe dukkan layukan da suka gaza hada lambobinsu da lambar ta NIN bayan cikar wa’adin da ta dibar musu.

Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "An tsawaita wa'adin hada nambar NIN da layukan wayan salalu"

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies