Gwarzon dan wasan Sevilla Kanouti zai gina masallacin da ba'ayi kamarsa ba a shekaru 700, cikin birnin Sevilla
Tsohon dan wasan na Sevilla da Mali, na shirin gina masallaci da ba ayi irin sa ba a spaniya cikin shekaru dari bakwai (700yrs).
Cikin shirinsa na gina kata faren masallacin Frédéric Omar Kanouti ya kaddamar da gidauniyarsa ta kafar yanar gizo, in da yayi nasarar tara kudi har dala miliyan daya "$1 million",. Dan wasan na Faransa mai asalinsa da mali, wanda ya taka leda a Sevilla FC, ya bayyana wannan cigaban ne a ranar talata da ya gabata.
Cikin shirinsa na gina kata faren masallacin Frédéric Omar Kanouti ya kaddamar da gidauniyarsa ta kafar yanar gizo, in da yayi nasarar tara kudi har dala miliyan daya "$1 million",. Dan wasan na Faransa mai asalinsa da mali, wanda ya taka leda a Sevilla FC, ya bayyana wannan cigaban ne a ranar talata da ya gabata.
Nagode muku kuma Allah ya biyaku duk wanda suka bada gudumawarsu cikin neman wannan gidauniyar.
Frédéric Kanouti ya sanar da sakon nan na godiya ta shafin sa na Twitter.
An sanar da cewa aikin ginin da gidauniyar tasa zai yi, zai hada masallacine da kumar cibiyar al'adu da zai gina wa musulman na Sevilla wanda shi zai kasance irinsa ta farko cikin shekaru dari bakwai. '700yrs'.
Kanouti Wanda ya shiga musulinci a lokacin yana da shekaru ashirin, ya sanar wa kafar yada labari ta Aljazeera lokacinda
" na shigo birnin Sevilla na tadda samun masallaci na da matukar wahala, har sai in na tambayi muta.
Yace Sevilla nada yawan musulmai sama da dubu talatin wanda ya hada da Spaniyawa da suka musulunta, mutanen Algeria, Morocco, Senegal da kuma 'yan asalin Mali.
Kafin ya kaddamar da gidauniyar tara wannan kudi da jama'a, a shekar dubu biyu da bakwai "2097" Kanouti ya biya kudin wani gu da musulmai ke salla agun lokacin ana dab da rufewa, sabo da kudin hayarsu ya kusa yayi expire, amma gidauniyar nan yanzu zai taimaka gun samarmusu da masallaci ta dindindin.
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Gwarzon dan wasan Sevilla Kanouti zai gina masallacin da ba'ayi kamarsa ba a shekaru 700, cikin birnin Sevilla"
Post a Comment