Duk wata mazauna kauyukan katsina na biyan 'yan bindiga haraji
Wasu al'umman kauyukan jihar katsina A kokarinsu na tsira da rayuwarsu da mutumcinsu, dake kananan hukumomi takwas na Jihar, wadanda mahara suka sa a gaba, sun shiga wata yarjejeniya da maharan inda suke biyansu wasu kudade na haraji duk wata.
Wani mai fashin baki na harkokin yau da kullum, Dakta Muttaka Darma, ne ya tabbatar da hakan a wata hira da aka yi da shi, inda ya bayyana cewa al’ummar kauyukan suna biyan kudaden da suka wuce Naira 150,000 duk watan duniya.
Daga cikin mutanan da suka kasa biyan wannan harajin suna tsirewa daga kauyukan don tsira da rayuwarsu, haka nan suke tsirewa su bar go
An fi samun afkuwar wannan lamarin a kananan hukumomin Faskari, musamman kauyukan Unguwar Tsamiya, Birnin Kogo, Bangi, Kahi da Raba.
Dakta Darma ya bayyana cewa; yanayin ya kai ga wasu daga cikin al’ummar kauyukan suna tsirewa don ceton rayukansu, saboda dalilin gaza biyan kudin, ko yawan kudin, inda wasu gungun na maharan suke karbar kudin da ya wuce Naira 150,000.
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Duk wata mazauna kauyukan katsina na biyan 'yan bindiga haraji"
Post a Comment