Za'a kuma garkame kananan hukumomi 18 -rahoton NCDC
NCDC ta kuma sanar Kananan Hukumomi 18 na kasar nan da su ke kumshe da jimillan kashi 60 na wadanda su ka kamu da annobar Korona suna fuskantar sake shiga karo na biyu na dokar kulle, Kwamitin ko-ta-kwana na Shugaban kasa a kan yakan annobar Korona ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Sai dai a wannan karon Gwamnonin Jihohi da aaakuma Kananan hukumomin da wadannan kananan hukumomin suke ne za su kula da yanda dokar kullen za ta yi aiki.
Shugaban kwamitin shugaban kasan, Boss Mustapha, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a bayan da ya gana da shugaban kasa inda ya ba shi bayanin halin da ake ciki a karshen makwanni hudu da sassauta dokar kullen, ya ce “Dangane da dokar kulle, mun gano kananan hukumomi 18 daga cikin kananan hukumomi 774 na kasar nan wadanda suke da mafiya yawan wadanda suka kamu da cutar ta korona, wadanda kuma suke kunshe da kashi 60 na jimillan mutane 24,077 na wadanda suka kamu da cutar a kasar nan bakidaya.
Dalilin kuwa sake mayar da dokar kullen a kansu shi ne daukan wasu matakai na musamman a wuraren a karkashin kulawar Jihohi da kananan hukumomin da suke. Wanda sam wannan ba hakkin gwamnatin tarayya ne ba, aiki ne da ya hau kan Jihohi da kuma kananan hukumomi.
Mustapha yana tare da rakiyar Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire, babban jami’in tsara aikin kwamitin Dakta Sani Aliyu da babban daraktan hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu, a ziyarar yin bayanin halin da ake cikin ga shugaban kasa.
Da yake yin karin haske dangane da sake kakaba dokar kullen a wancan kananan hukumomin, Dakta Sani cewa ya yi: “Wasu daga cikin wannan kananan hukumomin suna da matsala ce wacce ke da dangantaka da wuraren da suke, sannan kuma ba su da wata tabbatacciyar kan iyaka. Za mu aike da tantancewar da zaran mun kammala wannan aikin.
“Takaita zirga-zirga a wadannan kananan hukumomin daya ne kawai daga cikin matakan da za mu sanya a wadannan wuraren a matsayin wuraren da muka gano mafiya hatsari.
“Za mu kara yawan aikin gwaji a wadannan wuraren sannan za mu inganta wuraren kebe duk wanda aka gano cutar a tare da shi, domin tabbatar da mun wayar da kan jama’a yanda ya kamata.
“Don haka takaita zirga-zirga a cikinsu wani bangare ne kawai na hakan. Sannan a wasu kananan hukumomin mun san yin hakan mawuyacin abu ne. Mun san kananan hukumomin da yin hakan ba zai yiwu ba.
Ga Jerin Kananan Hukumomin Da Abin Zai Shafa Nan A kasa da yawan masu dauke da cutar a cikin su ya zuwa ranar 2 ga watan Yuni, kamar yanda rahoton hukumar ta NCDC ya nuna:
Mainland (1,274)
Abuja Municipal (536)
Mushin (458)
Eti-Osa (403)
Tarauni (248)
Katsina (242)
Alimosho (239)
Maiduguri (167)
Kosofe (175)
Dutse (170)
Ikeja (168)
Nassarawa (152)
Oshodi/Isolo (132)
Apapa (131)
Amuwo Odofin (129)
Oredo (126)
Bauchi (114)
Lagos Island (111)
Surulere (110) and
Ado Odo/Ota (107).
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Za'a kuma garkame kananan hukumomi 18 -rahoton NCDC"
Post a Comment