Ansa dokan hana taba dakin ka'aba ga mahajjatan da zasuyi bana.



A hajin bana da za'a gudanar Hukumomin kasar Saudiyya masu kula da masallatai biyu masu alfarma, sun sake sabunta wallafar ka’idojin da suka shata wanda za a kiyaye yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Wadannan ka’idojin kamar yadda mahukunta suka shar’anta, shi ne bai wa mahajja kariya daga cutar Korona tare da dakile yaduwar cutar a yayin sauke farali.

Jigo cikin sabbin ka’idojin da aka shar’anta, shi ne haramtawa Mahajjata kusantar dakin Ka’abah ballantana har ta kai ga shafar wani sashe na jikinta ko kuma damfara kirji da hannu kamar yadda aka saba.

Hukumomin sun shaidawa maniyyatan bana cewa, babu maganar shafar Dutsen Hajarul Aswad, wanda ya ke manne a kusurwar da ake fara daukar haramar dawafi.

Kamar dai yadda addinin Islama ya tanada, ana shafar Dutsen ne yayin da za a fara kowane nau’i na dawafi sannan a sumbaci hannun da aka taba dutsen da shi.



Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "Ansa dokan hana taba dakin ka'aba ga mahajjatan da zasuyi bana."

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies