Meya sa ake samun bambancin albashi tsakanin ma'aikata a Nigeria


arewatab

Wani abu dake bani mamaki da kasar mu Nigeria shine yadda ake samun wawakeken gibi na bambamcin albashi a tsakanin ma'aikatan gwamnati da suka Sami aiki a mabambamtan wurare. 

Alal misali idan muka Gama digiri lokaci daya watakila ma ajin mu daya, ba mamaki ma nafika kokari a ajin, kai watakila ma da muka kammala nafi ka samun sakamako Mai inganci, Amma idan ka Sami aiki a NNPC ko CBN( inda ba kasafai irin mu yamu bayi ke dace da irin wadannan wurare ba) ni kuma na yi dace na samu a wata makarantar sakandare a matsayin ticha, koma wata kwalejin Fasaha a matsayin lakcara, shikenan rayuwar mu ta sauya, ka zama hamshaki ni kuma na zama ba yabo ko fallasa a duniyance.

Babban abin da nake son fito dashi anan shine, Koda muna aiki a karkashin gwamnati daya Amma bambamcin wurin aiki zai nuna bambamcin albashi, kuma tazarar ba karama bace.

Na kasa gane hikimar haka, nayi zaton samun shugaban mu na yanzu me gaskiya zai duba irin wadannan matsaloli domin daidai ta wa, domin yanzu da wurin aiki ake dora ka a sikelin rayuwa Maimakon ingancin karatun ka.

Ban Sani ba ko sauran kasashen ma Haka ake yi, amma Koda Haka ake a kasashen ketare, a kasar mu Nigeria ya kamata ace an duba domin galiban mutanen da ba a irin wadannan ma'aikatu suke aiki ba albashin su baya kai su mikati, sai dai a karasa da Kara Kara ko kuma kame kame tsarkin maza, wasu kuma idan suka Sami damar cin rashawa shikenan, sai kaga mutum albashin sa, bai taka Kara ya karya ba, amma idan kaji ana kirga kadarorinsa Sai kasha mamaki.

Ya kamata mahukuntan mu su sake nazari Musamman ma a wannan zamani da talakawa ke ganin chanji suka zabo, domin idan ba'a sauya irin wadannan tsare tsare ba, tabbas ta'adanci da sace sace da rashawa bazasu gushe ba, Dan haka maimakon hukumar su Magu tayi ta farautar barayi, dacewa yayi a fara magance matsalar rashin adalci a tsakanin mutanen kasar.

Ni bance kowa Sai ya zama daya ba, Amma irin wannan bambamcin bashi da dalili.

Allah ya bamu ikon gyara kura kuran mu.

Rubutu Ra'ayin 

#Nasisu Salisu Zango

Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "Meya sa ake samun bambancin albashi tsakanin ma'aikata a Nigeria"

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies