Majalisar dinkin duniya ta amince da tabar wiwi a matsayin magani

arewatab


Duk da cewa an amince da amfani da wiwi don dalilai na waraka (magani), har yanzu ana ɗaukar sa a matsayin "abubuwan da ke da matukar haɗari ko kuma abubuwan da ake amfani dasu ba bisa ka ida ba" wanda ya haɗa da opium, hodar iblis, da kuma oxycontin. 

Tsawon shekaru 59, wiwi ya kasance cikin jerin abubuwan da ake danganta su da kwayoyi masu hadari (opioid), amma yanzu an cire shi daga rukunansu, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da karfafa amfani da shi don dalilai na kiwon lafiya. 

Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da magunguna masu guba (CND) ya gudanar da kuri’a kan lamarin, wanda ya samu kuri’u 27 da suka goyi bayan sake tantancewa sannan 25 suka nuna adawa da lamarin, yayin da kuri'a guda kuma bai goyi baya ko adawa dashiba. 

Duk da cewa an amince da amfani da wiwi don dalilai na waraka (magani), har yanzu ana ɗaukar sa a matsayin "abubuwan da ke da matukar haɗari ko kuma abubuwan da ake amfani dasu ba bisa ka ida ba" wanda ya haɗa da opium, hodar iblis, da kuma oxycontin. 

Hukumar ta WHO, wacce ke da alhakin kimanta kimiyanci game da abubuwan da za a iya amfani da su na warkewa da cutarwar da shan kwayoyi ke haifarwa a karkashin ka'idojin kasa da kasa, ya dogara ne da binciken da ya tabbatar da fa'idodin ka'idojin aiki na wiwi wajen magance cutar Parkinson, sclerosis, epilepsy, radadi da ciwon daji. 

Kimanin ƙasashe 50 sun riga sun fara shirye-shiryen amfani dashi a matsayin magani, ciki har da Argentina waɗanda suka yanke shawarar halatta noman wiwin a watan Nuwamba don siyar da mayinshi, yin man shafawa da sauran wasu abubuwa da ake da tsirre don dalilai na waraka.

Related Articles

I am the CEO And Founder of www.arewatab.com.ng

Subscribe Our Notification

0 Comments to "Majalisar dinkin duniya ta amince da tabar wiwi a matsayin magani"

Ads before post

Ads inside post

Ads under comment box

Ads after related movies