Haaland ya bayyana inda yake son taka leda nan gaba
Manyan kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Turai da suka hada da Barcelona na neman dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Haaland,
Yayin da ake ta fade fade makomarsa dan taba cewa uffun ba, sai dai a wannan karon ya fidda sakon da ya fito karara fiye da kowane lokaci.
"Zan taka leda a nan Spain," furucin da yayi lokacin da aka tambaye shi inane kulub na gaba da zai kasance, a cewar Diario AS.
Erling Haaland ya ci gaba da ba da haske kan makomarsa, kuma komai ya bayyana ba zai ci gaba da zama a Jamus ba bayan wannan kakar.
Lokacin da yake magana da magoya bayansa akan titi a Marbella ya sanarwa magoya bayan nasa cewa Ya zabi Spain ne a matsayin inda zai huta na ‘yan kwanaki kafin a dawo gasar lig ta Jamus daga hutu.
Kafofin yada labaran Jamus sun ruwaito cewa yanzu Dortmund ta ba Haaland wa'adin na sanin matsayarsa domin suma da wuri-wuri su san wace irin shiri da zasu wadda zai taimakama su.
A cewar Bild, kudin sakin Haaland Yuro miliyan 75 ne. Dukda Barça na da matsalolin kuɗi amma suna suna kokarin yadda zasu mallaki dan wasan
Related Articles
Subscribe Our Notification
0 Comments to "Haaland ya bayyana inda yake son taka leda nan gaba"
Post a Comment